Mutane 3 sun mutu yayinda mota ya fada a kogin Delta

Mutane 3 sun mutu yayinda mota ya fada a kogin Delta

Mutane uku ne suka mutu sanadiyar hatsari bayan fadiwar mota mai kirar Toyota Land Cruiser Prado cikin rafin Abarho a Okuokoko/Agbarho karshen hanyar gabashin yamma, a Arewacin karamar hukumar Ugheli dake jihar Delta.

Mutane shida ne suka kasance cikin motar yayinda hatsarin ta auku da misalin karfe 3:30 na yamma a ranar Sati.

Sannan uku daga cikin matafiyan, hade da direban sun tsere daga motar mai lamba Abuja DK 653 ABC, an rahoto cewa sauran mutane ukun sun mutu a hatsarin.

Daya daga cikin wadanda suka rayu, wanda bai bayyana kansa ba, ya fadawa jaridar PUNCH Metro a ranar lahadi a lokacinda ta ziyarci inda lamarin ya auku cewa dan uwansa ya sauka a lokacin da ya lura motar ta samu yar matsala.

Mutane 3 sun mutu yayinda mota ya fada a kogin Delta
Mutane 3 sun mutu yayinda mota ya fada a kogin Delta
Asali: Original

Ya bayyana cewa dukkan wadanda ke cikin motan sun kasance maza ne kuma suna a hanyar dawowa daga jihar Bayelsa ne, inda suka tafi gyaran daya daga cikin motocin kamfaninsu.

Ya kara da cewa matafiyan sun kasance kanikawa da masu gyaran wutar lantarki.

Sun kasance ma’aikatun kamfanin sadarwa, mallakin wani Cif Solomon Oloto.

Wanda ya tsiran ya bayyana matattun a matsayin Mista Jiwere Oloto wanda ya kasance dan uwa ga mai kamfanin, Musa a matsayin makani; da kuma Lucky a matsayin mai gyaran wutar lantarki.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wasu garuruwa a yankin Plateau ta arewa karkashin jagorancin kungiyar Berom Educational and Cultural Organization (BECO) sun bayyana cewa sun rasa kimanin mutane 300 wadanda mafi akasarinsu mata ne da yara cikin watanni hudu da suka gabata.

KU KARANTA KUMA: Dan kasuwa ya kawo cikas a hukuncin APC kan Buhari, ya shiga takarar kujeran shugaban kasa a jam’iyya mai mulki

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa a ranar Alhamis, 13 ga watan Satumba sun roki kasashen waje das u sanya baki wajen kawo karshen hare-haren a garuruwansu.

Sun yi korafin cewa mace-mace ya afku ne tsakanin watan Yuni zuwa Satumba a kananan hukumomin Barkin-Ladi da Riyom.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel