Siyasar Kano: Labarin rayuwar siyasar Dr. Nasiru Yusuf Gawuna

Siyasar Kano: Labarin rayuwar siyasar Dr. Nasiru Yusuf Gawuna

Ana sa rai kwanan nan Majalisar dokokin Jihar Kano ta tabbatar da Dr. Nasir Yusuf Gawuna a matsayin Mataimakin Gwamnan Jihar Kano.Yanzu dai mun ji cewa har an aika sunan sa zuwa Majalisar Jihar.

Don haka ne mu ka kawo abubuwan da ya kamata ku sani game da wanda ake sa rai ya zama Mataimakin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a Kano wanda rikakken ‘Dan siyasa ne kuma kasurgumin Attajiri.

Siyasar Kano: Labarin rayuwar siyasar Dr. Nasiru Yusuf Gawuna
Siyasar Kano: Labarin rayuwar siyasar Dr. Nasiru Yusuf Gawuna
Asali: Facebook

Nasiru Gawuna ya zama babban 'Dan adawar Kwankwaso daga baya inda kuma zai dare kan kujerar Mataimakin Gwamna bayan Farfesa Hafiz Abubakar wanda ke tare da Sanata Kwankwaso ya bar kujerar.

1. Shugaban Karamar Hukuma

Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya rike Shugaban Karamar Hukumar Nasarawa a lokacin Malam Ibrahim Shekarau yana Gwamnan Kano. A lokacin mutane sun tabbatar da cewa Gawuna yayi aiki a Nasarawa.

2. Kwamishina a lokacin Kwankwaso

A lokacin Gwamna Rabiu Kwankwaso ne aka nada Nasiru Gawuna a matsayin Kwamishi a Jihar Kano. Gawuna yana da mutane da-dama musamman a Yankin sa na Nasarawa a cikin Birnin Kano.

KU KARANTA: Wasu manyan ‘yan siyasa a Kano sun yi mubaya’a ga Kwankwasiyya

3. Kwamishina a lokacin Ganduje

Nasiru Gawuna yana cikin wadanda Ganduje ya tafi da su a mulkin sa ya kara nada sa Kwamishinan noma. Gwamna Abdullahi Ganduje ne yayi wa Kwankwaso Mataimaki a lokacin yana mulki.

4. Neman kujerar Sanatan Kano

Kafin yanzu dai Kwamishinan ya fara hangen doke Sanata Kano ta tsakia Rabiu Kwankwaso. Gawuna ya shirya takarar Sanata a APC kafin tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau ya dawo jam’iyyar.

5. Shugaban Kungiyar YFSN

Dr. Gawuna ya taba rike shugabancin Kungiyar YSFN watau “Youth Sports Federation of Nigeria” ta Matasan ‘Yan wasan da ke Najeriya. Gawuna mutum ne mai matukar son kwallon kafa.

Kwanaki kun ji Rabiu Musa Kwankwaso ya kai wa Janar Ibrahim Babangida ziyara a gida. ‘Dan takarar Shugaban kasan na PDP yayi kus-kus da IBB ne inda ya nemi albarka a zabe mai zuwa na 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel