Yanzu-yanzu: Ministan kudi, Kemi Adeosun, ta yi murabus

Yanzu-yanzu: Ministan kudi, Kemi Adeosun, ta yi murabus

Ministar kudin shugaba Muhammadu Buhari ta yi murabus daga gwamnatinsa, jaridar Daily Trust ta bada rahoto.

Abinda bai bayyana ba shine ko ta mika takardan murabus din ta shugaba Buhari.

Game da majiyar, Kemi Adeosun ta yi murabus ne bisa ga zargin rashin yin bautar kasan NYSC da ya wajaba kan kowani matashin Najeriya sannan kuma ta samu kwalin bautar na bogi.

Ministan ta yi murabus ne bisa ga yadda aka matsa mata lamba kuma yadda abin zai shafi zaben shugaba Buhari a 2019.

Yanzu-yanzu: Ministan kudi, Kemi Adeosun, ta yi murabus
Yanzu-yanzu: Ministan kudi, Kemi Adeosun, ta yi murabus
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Kalli takardun kammala karatun minista Kemi da shaidar NYSC din ta na karya

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa hakan na zuwa ne shekaru da yawa bayan ta kammala jami’a.

Dokar Najeriya ta tanaji hukunci ga mutumin da duk ya ki zuwa aikin bautar kasa da gangan matsawar dai bai cika shekaru 30 ba.

Takardun karatun Kemi da jaridar Premium Times ta wallafa sun nuna cewa hukumar ta ba ta takardun shaidar yafe mata zuwa bautar kasa a shekarar 2009, a bisa yawan shekaru.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel