Iko sai Allah: Wata amarya ta haihu awa 2 kafin daurin aure a Najeriya

Iko sai Allah: Wata amarya ta haihu awa 2 kafin daurin aure a Najeriya

- Wata amarya ta haihu awa 2 kafin daurin aure a Najeriya

- Amaryar sunan ta Misis Chinezu Adeolisa, mijin kuma sunan sa Mista Odeolisa

- Lamarin ya auku ne a garin auku a garin Awo Idemili na jihar Anambara

Wani lamari mai cike da sarkakkiyar ban al'ajabi ya auku a garin Awo Idemili na jihar Anambara dake a shiyyar kudu maso gabashin kasar nan inda amarya ta haifi sambalelen saurayi kimanin awa biyu kafin a daura mata aure.

Iko sai Allah: Wata amarya ta haihu awa 2 kafin daurin aure a Najeriya
Iko sai Allah: Wata amarya ta haihu awa 2 kafin daurin aure a Najeriya
Asali: Facebook

KU KARANTA: Sojin Saman Najeriya sun samu galaba akan 'yan Boko Haram

Ita dai amaryar mai suna Misis Chinezu Adeolisa ta bayyana wa duniya farin cikinta na samun sankacecen jariri a ranar ɗaurin aurenta da rabin ranta Mista Odeolisa.

Legit.ng ta samu haka zalika cewa da yake tsokaci game da lamarin, angon Mista Odeolisa ya bayyana wannan al'amari da cewa daɗi kan daɗi ne. Wato alhairai biyu, a lokaci guda.

Majiyar mu dai ta labarta mana yadda lamarin ya faru inda tace abin ya farune awoyi kaɗan kafin a fara shagalin ɗaurin auren, sai kawai nakuda ta kama amaryar. Nan da nan aka mika ta asibiti inda ta haife lafiya, ta samu ɗanta namiji.

A wani labarin kuma, Kamfanin sadarwar nan na MTN a Najeriya ya maka babban bankin na Najeriya watau Central Bank of Nigeria (CBN), da kuma Antoni Janar na kasar kuma ministan shari'a a gwamnatin shugaba Buhari kotu yana neman a bi masa hakkin sa.

Kamar dai yadda muka samu, shi dai kamfanin a ranar Litinin din da ta gabata ne ya shigar da karar kotu a garin Abuja, yana kalubalantar matakin da gwamnatin Najeriya ta kakaba masa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel