Ba lafiya: An nemi wani babban soja a Najeriya - Manjo Janar Idris Alkali an rasa

Ba lafiya: An nemi wani babban soja a Najeriya - Manjo Janar Idris Alkali an rasa

- An nemi wani babban soja a Najeriya - Manjo Janar Idris Alkali an rasa

- Kungiya CUPS ce ta fara sanar da hakan

- Manjo Janar Alkali dai ya bace akan hanyar sa ta zuwa Bauchi daga Abuja

Wani labari mai matukar tayar da hankali da muke samu daga majiyoyi da dama a nuni da cewa daya daga cikin hazikan sojojin Najeriya kuma Manjo Janar a gidan soja mai suna Manjo Janar Idris Alkali yayi batan dabo.

Ba lafiya: An nemi wani babban soja a Najeriya - Manjo Janar Idris Alkali an rasa
Ba lafiya: An nemi wani babban soja a Najeriya - Manjo Janar Idris Alkali an rasa
Asali: Facebook

KU KARANTA: An samu labarin halin da Sambo Dasuki yake a hannun DSS

Wata kungiya ce dai ta masu rajin tabbatar da mulkin demkradiyya da kuma kyakykyawan shugabanci mai suna CUPS a takaice ta fara sanar da hakan a shafin ta na dandalin sadarwar zamani na Facebook.

Legit.ng ta samu cewa kamar yadda majiyar ta mu ta bayyana, Manjo Janar Alkali dai ya bace ne akan hanyar sa ta zuwa garin Bauchi daga garin Abuja, babban birnin tarayya.

Sai dai kuma kamar yadda muka samu, kungiyar tace yau kimanin kwana hudu kenan dukkan lambobin sa basu shiga kuma har yanzu ba'a ji daga gare shi ba wanda lamarin yayi matukar tayar da hankulan 'yan uwa da abokan arzikin sa.

A wani labarin kuma, Jami'an sojojin saman Najeriya dake a cikin rundunar hadin gwuiwa ta Lafiya Dole dake yaki da 'yan ta'addan Boko Haram a shiyyar Arewa maso gabashin kasar nan sun sanar da samun gagarumar nasara a kan 'yan ta'addan a maboyar su dake a dajin Sambisa.

Kamar yadda muka smu, rundunar ta bayyana cewa ta samu yin galaba akan 'yan ta'addan ne tare kuma da yin fata-fata da ma'ajiyar makaman a dajin na Sambisa dake zaman mafaka gare su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel