Duk mai shaidar na taba satar ko da kwandala ce ya fito ya nuna kan sa - Atiku

Duk mai shaidar na taba satar ko da kwandala ce ya fito ya nuna kan sa - Atiku

- Duk mai shaidar na taba satar ko da kwandala ce ya fito ya nuna kan sa - Atiku

- Yace shi tun da yake bai taba satar kudin al'umma ba

- Yace duk yarfen siyasa ne kawai ake yi masa

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma mai neman tikitin takarar shugabancin kasar a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar yace shi tun da Allaha yayi shi bai taba satar ko da kwandala ba.

Duk mai shaidar na taba satar ko da kwandala ce ya fito ya nuna kan sa - Atiku
Duk mai shaidar na taba satar ko da kwandala ce ya fito ya nuna kan sa - Atiku
Asali: UGC

KU KARANTA: Shugaba Buhari yayi sabbin nade nade 4

Fitaccen dan siyasar haka zalika ya kalubalanci duk wani mai shaidar cewa ya taba karkatar da dukiyar al'umma ko kuma wata rashawa ko cin hanci da ya fito ya fallasa hakan a idon duniya.

Legit.ng ta samu cewa tsohon mataimakin shugaban kasar dai yai wannan shelar ne a garin Ado Ekiti, jihar Ekiti lokacin da yake jawabi ga 'yan jam'iyyar tasu ta PDP a cigaba da zagayen sada zumunci da yake yi.

Haka zalika Atiku Abubakar ya ce duk maganganun da ake yi na cewar bai da gaskiya ko kuma yana cin hanci ko rashawa tsabar adawa ce kawai ta makiya.

A wani labarin kuma, Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma mai neman tikitin takarar shugabancin kasar a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana wasu halaye da yake zargin shugaba Muhammadu Buhari yana da su da ka iya kawo barazana ga sahihancin zabukan 2019.

Majiyar mu ta tsinkayi fitaccen dan siyasar yana cewa "Shugaba Buhari wanda tsohon soja ne yana da kafiya da rashin jin shawara sannan kuma gashi yana da bala'in son mulki.

"Wadannan da ma wasu halayen sa ne yasa nike da shakku matuka game da yiwuwar samun sahihin zabe a karkashin kulawar sa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel