Wani gwamna a Najeriya ya roki Buhari ya yafewa barayin Najeriya

Wani gwamna a Najeriya ya roki Buhari ya yafewa barayin Najeriya

- Wani gwamna a Najeriya ya roki Buhari ya yafewa barayin Najeriya

- Yace shari'o'in da ake yi kan cin hanci da rashawa sun yi yawa

Gwamnan jihar Ebonyi da ke a kudu maso gabashin Najeriya mai suna David Umahi yayi kira ga gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari da su duba yiwuwar yafewa dukkan 'yan siyasar da ake zargi da laifin wawure dukiyar al'umma.

Wani gwamna a Najeriya ya roki Buhari ya yafewa barayin Najeriya
Wani gwamna a Najeriya ya roki Buhari ya yafewa barayin Najeriya
Asali: Facebook

KU KARANTA: Shugaba Buhari yayi wasu muhimman nade-nade 4

Mista David Umahi yayi wannan kiran ne a garin Abakalki, babban birnin jihar lokacin da yake jawabi a wurin bude wani taro game da cin hanci da kuma gyaran tarbiyya da da'ar mutanen jihar.

Legit.ng ta samu haka zalika gwamnan ya koka ne game da irin tarin shari'oin da suka shafi cin hanci da rashawa dake a gaban alkalai a kotunan Najeriya inda ya zargi gwamnatin tarayyar da dauko dala ba gammo.

Daga nan ne sai ya shawarci gamnatin da ta yafewa kowa sai ta sake daga farko ta bude sabon shafi.

A wani labarin kuma, Jami'an 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Delta dake a yankin kudu maso kudancin kasar nan sun tabbatar da sace wani babban malamin addinin kirista ajihar mai suna Rabaran Fada Christopher Ogaga a garin Oviri-Okpe dake a karamar hukumar Okpe.

Kamar dai yadda muka samu, Kwamishinan 'yan sandan jihar Alhaji Muhammad Mustafa shine ya sanar wa da manema labarai hakan a garin Warri, daya daga cikin manyan garuruwan dake a jihar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel