Babu wani tantancewa da za’a yiwa Saraki, Atiku, Kwankwaso da sauransu a yanzu

Babu wani tantancewa da za’a yiwa Saraki, Atiku, Kwankwaso da sauransu a yanzu

Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) yayi bayanin dalilin da yasa ba’a kaddamar da wani kwamiti da zai tantance yan takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar ba tukuna.

Baya ga yan takarar kujerar shugaban kasa, jam’iyyar bata ambaci wani kwamiti da zai yi duba ga takardun sauran yan jam’iyya.

Tuni dai yan takara da dama sun yanki fam din takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar inda suke jira a kaddamar da kwamitin.

Daga cikin yan takaran da suka yanki fam dinsu sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso, Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, da kuma gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo.

Babu wani tantancewa da za’a yiwa Saraki, Atiku, Kwankwaso da sauransu a yanzu
Babu wani tantancewa da za’a yiwa Saraki, Atiku, Kwankwaso da sauransu a yanzu
Asali: Twitter

Har ila yau akwai tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, tsohon ministan ayyuka na musamman, Alhaji Tanimu Turaki; tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau; Attahiru Bafarawa da kuma Dr Ahmed Datti.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Kada Yan sanda da INEC su sanya baki a zabin mutane - Buhari

Babban sakataren labaran jam’iyyar, Mista Kola Ologbondiyan, ya fadama majiyarmu cewa a ranar Lahadi cewa babu laifi a cikin jinkirtawan, cewa jam’iyyar zata gabatar da mambobin kwamitin ba da dadewa ba.

Ya bayyana cewa jam’iyyar ta mayar da hankali wajen siyar da fam dinta, cewa da zaran an kammala da wannan kwamitin masu ruwa da tsaki zata saki sunaye.

A wani lamari na daban, mun ji cewa alkalin alkalai kuma ministan shari’a, Mista Abubakar Malami ya kalubalanci hukuncin babban kotun tarayya na sauraron karar dake bukatar a dakatar da tsige Dr Bukola Saraki a matsayin shugaban majalisar dattawa.

Ministan shari’an ya bukaci babban kotun da tayi watsi da karar da tsoffin sanatocin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Rafiu Adebayo da Isa Misau suka shigar a gabanta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel