Zaben 2019: Kada Yan sanda da INEC su sanya baki a zabin mutane - Buhari

Zaben 2019: Kada Yan sanda da INEC su sanya baki a zabin mutane - Buhari

- Shugaban kasa Buhari yayi jan kunne akan zaben 2019

- Ya gargadi jami'an tsaro da hukumar INEC da su bar mutane suyi zabin ransu

- Buhari yayi alkawarin gabatar da zabe mai sahihanci a karkashin gwamnatinsa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fadama rundunar yan sandan Najeriya, hukumar zabe mai zaman kanta da sauran hukumomin tsaro a kasar da su bari yan Najeriya su yi zabin ransu a zaben 2019 ba tare da kowani irin barazana ba.

Shugaban kasar ya bayyana cewa shi ma ya amfana daga zaben gaskiya da amana, bayan ya sha kaye sau uku, baya tsoron yin zabe na gaskiya da amana a shekara mai zuwa.

Ya sake ba da tabbacin jajircewarsa domin tabbatar da cewa zaben 2019 a karkashin gwamnatinsa ta zamo na gaskiya da amana.

Zaben 2019: Kada Yan sanda da INEC su sanya baki a zabin mutane - Buhari
Zaben 2019: Kada Yan sanda da INEC su sanya baki a zabin mutane - Buhari
Asali: Facebook

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Buhari ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda kafofin watsa labarai ke rikon lamarin rikicin makiyaya da manoma a kasar sannan ya bayar da shawarar cewa kafofin watsa labarai suyi kokari su nemi sanin tarihin abun.

KU KARANTA KUMA: 2019: ‘Yan Najeriya sun yiwa Atiku shagube a kan zubar da hawaye

Da yake Magana a wani taron tattaunawa day an Najeriya a Beijing, China a jiya Buhari yayi alkawarin cewa yan Najeriya da suka kai matsayin zabe za’a bari su zabi san ransu.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Buhari ya amince da wasu sabbin nade-nade guda hudu da suke da alaka da kamfanin nan na gwamnatin tarayya dake bugawa tare da tsare takardun sirri watau Nigerian Security Printing and Minting Company.

Kamar yadda muka samu, Shugaba Buhari din ya nada Alhaji Abbas Umar Masanawa a matsayin babban manajan Daraktan kamfanin tare kuma da wasu manyan daraktocin sa su biyu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel