Kutungwuila: Ana ta shirya makarkashiyar maido da Lawal Daura aiki ta karkashin kasa

Kutungwuila: Ana ta shirya makarkashiyar maido da Lawal Daura aiki ta karkashin kasa

- Ana ta shirya makarkashiyar maido da Lawal Daura aiki ta karkashin kasa

- Sabbin tsare tsaren da sabon shugaban DSS yake kawo wa na bata ma wasu rai

- Lawal Daura na da uwa a bakin murhu

Wasu rahotannin da muke samu daga majiyoyin mu suna nuni ne da cewa wasu makusantan Shugaba Muhammadu a fadar shugaban kasa sun nan sun yi nisa wajen shirya kutungwuilar maido da Lawal Daura da aka kora aikin sa.

Kutungwuila: Ana ta shirya makarkashiyar maido da Lawal Daura aiki ta karkashin kasa
Kutungwuila: Ana ta shirya makarkashiyar maido da Lawal Daura aiki ta karkashin kasa
Asali: Facebook

KU KARANTA: Sojin saman Najeriya sun yi wa 'yan Boko Haram mummunar illa

Majiyar dai wadda jaridar Vanguard tace kusa take da shugaban kasar ta ce makusantan na Shugaba Buhari basu jin dadin irin sauye-sauyen da sabon shugaban riko na hukumar tsaron farin kayan na DSS mai suna Mathew Seiyefa yake yi.

Legit.ng ta tuna cewa a watan da ya gabata ne dai mukaddashin shugaban kasa a wancen lokacin ya tsige Lawal Daura daga mukamin sa ya kuma sa aka tsare shi bayan kutsen da jami'an 'yan sandan farin kaya suka yi wa majalisar dattawa.

Lawal Daura dai kamar yadda muka samu ya fito ne da garin Shugaban kasa na Daura kuma ana kyautata zaton yana da daurin gindi da kuma fada mai karfi a wajen shugaban kasar.

A wani labarin kuma, Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma fitaccen dan siyasa dake neman tikitin takarar shugabancin kasar nan a shekarar 2019 ya bayyana cewa sam mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo bai ma gama fahimtar Najeriya ba.

Atiku dai yana maida martani ne game da kalaman Osinbajo din da yayi a lokacin da yake tattaunawa da wasu 'yan Najeriya a kasar Amurka inda yace wai sauya fasalin kasar baya daya daga cikin matsalolin Najeriya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel