Tsadar tikiti: Da alama APC za ta rasa yan takara a zaben fitar da gwani

Tsadar tikiti: Da alama APC za ta rasa yan takara a zaben fitar da gwani

- Rahotannin da ke yawo, na nuni da cewa jam’iyyar APC na iya rasa da yawa daga cikin wadanda suka nuna sha’awar tsayawa takara a karkashin jam’iyyar

- Hakan ya biyo bayan tsadar farashin tikitin tsayawa takara a kowane mataki sabanin kudin da jam’iyyar PDP ta sanyawa nata

- Rahotanni sun bayyana cewa yan takarar sun bukaci da a rage kudaden da aka sanya.

Yan takara a karkashin jam’iyyar APC na ci gaba da nuna dari-dari da shuwagabannin jam’iyyar, biyo bayan tsadar kudin tikitin tsayawa takara da jam’iyyar ta sanar.

Rahotannin da Legit.ng ta tattara a Abuja, a ranar asabar, na nuni da cewa yan takara a jam’iyyar, da suka nuna sha’awar tsayawa takara a matakin gwamna, majalisun dokoki na kasa da ma shugaban kasa, na bayyana damuwarsu bisa tsadar da tikitin yayi.

Rahotanni sun bayyana cewa yan takarar sun bukaci da a rage kudaden da aka sanya.

A baya bayan nan ne dai kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ta APC, ya fitar da kudin tikitin tsayawa takarar shugaban kasa akan Naira Miliyan 55, wanda ya haura Naira Miliyan 12 da jam’iyyar PDP ta sanyawa nata

KARANTA WANNAN: Ruwan sama ya rusa makabarta da hana mutane binne gawa a jihar Katsina (Hotuna)

Tsadar tikiti: Da alama APC za ta rasa yan takara a zaben fitar da gwani
Tsadar tikiti: Da alama APC za ta rasa yan takara a zaben fitar da gwani
Asali: Twitter

Wadanda suka bayyana sha’awarsu ta tsayawa takarar majalisun dokoki na jihohi a jam’iyyar, za su biya Naira miliyan daya dadubu dari, sabanin na jam’iyyar PDP da zasu biya Naira 600,000. Ya yin da yan takarar majalisun tarayya zasu sayi tikitin akan kudi N3.8m., sabanin na jam’iyyar PDP da zasu biya N1.5m.

A bangaren masu sha’awar tsayawa takara a matakin majalisar dattijai, jam’iyyar ta APC ta sa kudin tikitin akan N8.5m, sabanin N3.5m da jam’iyyar PDP ta sanyawa yan takarar majalisar dattijai a jam’iyyar.

An bukaci masu sha’awar tsayawa takarar gwamna a jam’iyyar APC da su biya kudin tikiti N22.5m sabanin N6m da PDP ta sanyawa tikitin tsayawa takarar gwamnan a jam’iyyarta.

Wani mamba a kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC a matakin kasa, wanda ya zanta da manema labarai dangane da rade-raden da ke yawo na wasu yan takara a jam’iyyar na iya sulalewa saboda tsadar tikitin, ya ce jam’iyyar na akan bakanta, ba zata rage farashin komai ba.

Wani tankarar majalisar tarayya a karkashin jam’iyyar ya ce tsadar tikitin ba zata lalata shirye shiryen da aka rigaya akayi ba, sai dai zasu yi zama na musamman, don tsara yadda lamarin zai kasance.

“Zamu bukaci jam’iyyar da ta sauko da wannan farashin nata, ko kuma ta fuskanci janyewa daga mutane da dama, don kuwa tsadar tikitin ta yi yawa,” a cewar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel