Fitar da gwani: APC zata gamu da matsala idan ba ta bi tsarin kato-bayan-kato ba - Sanata

Fitar da gwani: APC zata gamu da matsala idan ba ta bi tsarin kato-bayan-kato ba - Sanata

- APC zata gamu da matsala idan ba ta bi tsarin kato-bayan-kato ba

- Sanata Kabiru Garba Marafa na Zamfara ne ya ce haka

- Sanatan yana neman tikitin jam'iyyar don yin takarar gwamna a jihar

Sanata Kabiru Garba Marafa dake wakiltar mazabar jihar Zamfara ta tsakiya a zauren majalisar dattawan Najeriya ya yi hasashen tunkarowar babbar matsala a jam'iyyar su ta APC idan dai har bata bi tsarin gudanar da zaben fitar da gwani na kato-bayan-kato ba.

Fitar da gwani: APC zata gamu da matsala idan ba ta bi tsarin kato-bayan-kato ba - Sanata
Fitar da gwani: APC zata gamu da matsala idan ba ta bi tsarin kato-bayan-kato ba - Sanata
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Gwamnan Legas ya kama hanyar ficewa daga APC

Sanatan dai wanda ke neman tikitin jam'iyyar don yin takarar gwamna a jihar ya ce idan har jam'iyyar tayi fatali da tsarin a matakin jahohi to ta shirya zuwa kotu da ma faduwa zabe a shekarar 2019.

Legit.ng ta samu cewa Sanatan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake fira da wakilin majiyar mu ta wayar tarho a game da matsayar sa akan tsarin zaben da yake ganin ya dace jam'iyyar tabi wajen fitar da 'yan takarar ta a zabuka masu zuwa.

Idan dai ba'a manta ba Sanatan yana daya daga cikin 'yan jihar ta Zamfara da suka rika sukar salon mulkin gwamnan jihar Abdulaziz Yari musamman ma ta fannin yadda tsaro ya tabarbare.

A wani labarin kuma, Daya daga cikin fitattun 'yan siyasar Najeriya dake neman tikitin takarar shugabancin kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP Alhaji Sule Lamido ya roki 'yan jam'iyyar da su yi masa halacci musamman ma shi da bai taba fita daga jam'iyyar ba.

Alhaji Sule yayi wannan rokon ne a lokacin da yake zantawa da jiga-jigan jam'iyyar da za su gudanar da zaben fitar da gwani na jihar Nasarawa a cigaba da yawon zumuncin da yake yi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel