An kama wani malamin addini da ya shahara wajen yin zina da kananan yara a Najeriya

An kama wani malamin addini da ya shahara wajen yin zina da kananan yara a Najeriya

- An kama malamin addini da zina da kananan yara a Najeriya

- Babban malamin fasto ne a garin Abuja

- Hukumar nan ta NAPTIP ce ta kama shi

Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake yaki da masu safarar mutane da muzgunawa yara kanana da mata ta National Agency for the Prohibition of Trafficking in Persons, NAPTIP tace ta samu nasarar cafke wani malamin addinin kirista da laifin yin zina da 'yan mata.

An kama wani malamin addini da ya shahara wajen yin zina da kananan yara a Najeriya
An kama wani malamin addini da ya shahara wajen yin zina da kananan yara a Najeriya
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Wani dan sanda ya kashe dan tasi saboda Naira 10

Hukumar ta ce babban malamin wanda yake da shekaru 46 a duniya sun kama shi ne a garin Abuja babban birnin tarayya tare da kuma wasu mutanen su biyu.

Legit.ng ta samu cewa babban daraktan hukumar dake kula da harkokin bincike da sa'ido Mista Josiah Emerole shine ya sanarwa da manema labarai hakan a garin na Abuja.

Mista Josiah Emerole ya kara da cewa Faston yanzu haka ya wurin su suna cigaba da bicike kuma da zarar sun kammala za su mika shi hannun jami'an gwamnatin da suka dace.

A wani labarin kuma, Wani labari mai ban takaici da ya riske mu na nuni ne da cewa wani dan sanda kashe wani direban motar haya har lahira saboda cin hancin Naira 10 da ya ki bashi.

Kamar dai yadda muka samu, lamarin ya auku ne a garin MaiSamari a karamar hukumar Sardauna ta jihar Taraba inda 'yan sandan suka saka wani shinge suna tare ababen hawa har sai sun bayar da Naira 50 sannan su wuce.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel