An nada Sani Danja a matsayin jakadan kungiyar NFVCB

An nada Sani Danja a matsayin jakadan kungiyar NFVCB

- Kungiyar tantance fina-finai da bidiyo a kasa ta karrama Sani Danja

- An nada shi a matayin jakadan kungiyar ta NFVCB

- An bayyana bin doka da manufofin gwamnati a matsayin dalilin nada mai jakadancin kungiyar

Kungiyar tantance fina-finai da bidiyo a kasa (NFVCB) ta na jarumin shirya fina-finan Hausa na Kannywood kuma mawaki, Sani Danja a matsayin jakadanta.

Babban darakta na hukumar NFVCB, Alhaji Adedayo Thomas ne ya bayyana hakan a yau, Jumaá, 31 gwatan Agusta.

An nada Sani Danja a matsayin jakadan kungiyar NFVCB
An nada Sani Danja a matsayin jakadan kungiyar NFVCB
Asali: UGC

"Hukumar ma’aikatar ne suka zabe shi saboda ya nuna cewa yana tare da manufofin gwamnati. Hakan yasa shi kaiwa wannanmatsayin sanna kuma yazamo abun koyi ga sauran mutane,” inji Thomas.

Danja wadda ke shirin fito da sabuwar alban dinsa a kasuwa, yace awai bukatar mawaka su gabatar da ayyukansu ta hukumar tantancen fina-finai. “Ba wai sai an saci fasahar aikinka sannan ne zaka ara neman bin doka ba,”cewar shi.

KU KARANTA KUMA: 2019: Ban tsayar da kowa ba a kowani mukamin siyasa – Dogara

Sabon alban din mawakin na kunshe ne sakon soyayya da hadin kai da kuma sabon rawa mai taken “siren”.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel