Dandalin Kannywood: Tsabar sha'awa ce ta sa na shiga harkar fina finai - Inji wani jarumi
- Tsabar sha'awa ce ta sa na shiga harkar fina finai
- Jarumin sunan sa Garzali Miko
- Yace ya fara harkar fim din kusan shekaru 10 da suka shude
A kokarin mu na cigaba da kawo maku labaran da suka shafi masana'antar shirya fina-finan Hausa da ake yi wa lakani da Kannywood, yau ma gamu dake da wata fita da daya daga cikin fitattun jarumai kuma sabuwar fuska a masana'antar yayi da majiyar mu.

Asali: Facebook
KU KARANTA: Zan sakar wa 'yan luwadi da madgo mara in na zama shugaban kasa - Doland Duke
Jarumin dai ba boyayye bane ba ga mafiya yawa daga cikin masu sha'awa tare da bibiyar harkokin fina-finan Hausa din kuma wannan ba kowa bane ba face Garzali Miko.
Legit.ng ta samu cewa fitaccen jarumin kuma dan rawa ya bayyana cewa ya fara harkar fina-finan Hausa ne kimanin shekaru sama da goma da suka shude inda a da yake aikin bayar da haske kafin daga bisani ya kara samun matsayi a harkar.
Haka zalika jarumin ya bayyana cewa tsabar sha'awa ce kawai ta jefa shi cikin harkar shi yasa ma ya faro ta tun daga tushe watau a matsayin karami a harkar ya ya zuwa yanzu da ya soma zama fitacce kuma jarumi.
Garzali ya kuma kara da cewa akwai kalubale a harkar ta fim kamar dai sauran fannonin rayuwa da ma duk abinda dan Adam keyi wani lokaci a samu farin ciki wani lokaci kuwa a sami akasin haka.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng