Tantiran tsagerun Neja Delta sun yi barazanar dagulawa Shugaba Buhari lissafi
- Tsagerun Neja Delta sun yi barazana ga Shugaba Buhari
- Sun ce za su cigaba da kai hare-hare
- Sun yi kaca-kaca da jam'iyyar APC
Tantiran tsagerun nan na Neja Delta a karkashin wata gamayyar kungiyoyi da suka kira Coalition Niger Delta Agitators sun yi barazanar cigaba da kai sabbin hare-hare akan bututan mai dake a yankunan su idan dai har gwamnatin Buhari bata sake fasalin kasar nan ba.

KU KARANTA: Zamu kawo hari: Yan bindiga sun aika wasika zuwa garuruwa 4 a Arewa
Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban gamayyar kungiyoyin Mista John Duku ya fitar dauke da sa hannun sa a ranar Asabar din da ta gabata a garin Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.
Legit.ng ta samu cewa a cikin sanarwar, tsagerun sun yi Allah-wadai da irin salon mulkin jam'iyyar APC da sukace kwata-kwata yayi hannun riga da na demokradiyya tare da jan hankalin Shugaba Buhari da ya gaggauta biya masu bukatun su.
A wani labarin kuma, Yanzu haka dai harkokin tattalin arziki na cigaba da tabarbarewa yayin da baitul mali na Najeriya a babban bankin kasar watau Central Bank of Nigeria ya yi kasa da dalar Amurka miliyan 990 a cikin sati uku kacal da suka shude.
Wannan dai na kunshe ne a cikin rahoton da babban bankin ya fitar majiyar mu kuma ta Punch ta same shi a ranar Lahadin da ta gabata.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng