Wani babban ibtila'i ya afkawa hedikwatar 'yan Shi'a ta duniya

Wani babban ibtila'i ya afkawa hedikwatar 'yan Shi'a ta duniya

Wata gagarumar girgizar kasa mai girman digo shidda a ma'aunin karfin ta ta afkawa yammacin kasar Iran dake da iyaka da makwafciyar ta ta kasar Iraq da safiyar ranar Lahadi.

Kamar yadda muka samu girgizar kasar wadda ta mamaye kusan kilomita 26 a garin Javanrud dake a jihar Kermanshahta mutane sama da 200 ne suka jikkata.

Wani babban ibtila'i ya afkawa hedikwatar 'yan Shi'a ta duniya
Wani babban ibtila'i ya afkawa hedikwatar 'yan Shi'a ta duniya

KU KARANTA: Zanga-zangar dalibai ta ja an rufe wata jami'a a Arewa

Legit.ng ta samu cewa kasar Iran dai dake a yankin gabas ta tsakiya na zaman babbar hedikwatar musulmai mabiya darikar Shi'a kuma suna da'awar tabbatar da shari'ar muslunci ne kamar kasar Saudiyya.

A wani labarin kuma, Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun aika da sakon ban tsoro da razanarwa ga al'ummar garuruwa hudu a karamar hukumar Rabah ta jiha Sokoto dake da iyaka da jihar Zamfara inda suka sanar da su zuwan su a cikin 'yan kwanakin nan.

Majiyar mu ta Daily Nigerian dai ta bayyana cewa garuruwan da 'yan bindigar suka aikawa sakon sun hada da Ruwan Tsamiya da Kursa da Kaiwar Dawa da kuma Malela duk dai a karamar hukumar ta Raba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel