Yadda wani barawon wayar salula ya sha gwale-gwale a hannun sojin Najeriya

Yadda wani barawon wayar salula ya sha gwale-gwale a hannun sojin Najeriya

- Wani barawon wayar salula ya sha gwale-gwale hannun sojoji

- Barawon ya rasa ransa ta dalilin hakan

- Lamarin ya faru ne a jihar Filato

Wasu dakarun sojin Najeriya dake a wata runduna ta musamman dake aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar Filato sun kashe wani matashi mai shekaru 18 a duniya da gwale-gwale sakamakon zargin sa da akayi da satar wayar Salula.

Yadda wani barawon wayar salula ya sha gwale-gwale a hannun sojin Najeriya
Yadda wani barawon wayar salula ya sha gwale-gwale a hannun sojin Najeriya

KU KARANTA: Al'ummar wata jiha a Kudu sun yiwa Buhari alkawarin kuri'un su a 2019

Lamarin dai kamar yadda muka samu ya faru ne a karamar hukumar Bokkos ta jihar kuma matashin da ya rasa ransa sunan sa Amadu Atajan wanda bai dade da kammala karatun sa na makarantar gaba da Sakandire ba.

Legit.ng ta samu cewa al'ummar gari dai da ma kungiyoyi da dama sun nuna takaicin su game da lamarin sannan kuma suka bukaci gwamnati da ta gaggauta yin bincike da zummar hukunta duk masu hannu a ciki.

A wani labarin kuma, Dakarun sojin Najeriya dake fafutukar ganin sun kakkabe dukkan barbashin 'yan ta'addan Boko Haram sun sanar da samun nasarar kashe manyan kwamandojin 'yan ta'addan uku yayin wani artabu da sukayi da su a garin Bama.

Babban daraktan yada labarai da hulda da jama'a na rundunar, Texas Chukwu shine ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ya kuma rabawa manema labarai a ranar Juma'ar da ta gabata.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng