Yadda ta kaya da sojin Najeriya suka gabza fada da 'yan Boko Haram

Yadda ta kaya da sojin Najeriya suka gabza fada da 'yan Boko Haram

- Sojojin Najeriya da yan Boko Haram an gabza fada

- Sojojin Najeriya ne suka samu galaba

- Jami'in hulda da jama'a na sojojin ne ya shaida mana

Dakarun sojin Najeriya dake fafutukar ganin sun kakkabe dukkan barbashin 'yan ta'addan Boko Haram sun sanar da samun nasarar kashe manyan kwamandojin 'yan ta'addan uku yayin wani artabu da sukayi da su a garin Bama.

Yadda ta kaya da sojin Najeriya suka gabza fada da 'yan Boko Haram
Yadda ta kaya da sojin Najeriya suka gabza fada da 'yan Boko Haram

KU KARANTA: Kazamar zanga-zangar dalibai ta ja anrufe wata jami'a a Arewa

Babban daraktan yada labarai da hulda da jama'a na rundunar, Texas Chukwu shine ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ya kuma rabawa manema labarai a ranar Juma'ar da ta gabata.

Legit.ng ta samu cewa Texas Chuku ya kuma kara bayyana cewa sojojin sun samu galabar kwace muggan makamai daga hannun 'yan ta'addan da suka hada da bindigu uku kirar AK 47 da harsasai da dama.

A wani labarin kuma, Wasu dakarun sojin Najeriya dake a wata runduna ta musamman dake aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar Filato sun kashe wani matashi mai shekaru 18 a duniya da gwale-gwale sakamakon zargin sa da akayi da satar wayar Salula.

Lamarin dai kamar yadda muka samu ya faru ne a karamar hukumar Bokkos ta jihar kuma matashin da ya rasa ransa sunan sa Amadu Atajan wanda bai dade da kammala karatun sa na makarantar gaba da Sakandire ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel