Duniyar kimiyya: Masana sun tabbatar da gano wani abun mamaki a duniyar wata

Duniyar kimiyya: Masana sun tabbatar da gano wani abun mamaki a duniyar wata

- Masana sun gudanar da sabon bincike a duniyar wata

- Masanan sun gano abun mamaki

- Masanan sun ce akwai kankara mai yawa

A karon farko a tarihin duniya, masana ilimin kimiyyar sararin samaniya na kasar Amurka sun tabbatar da gano ruwa da kuma kankara a saman duniyar wata a wani binciken kwana-kwanan nan da suka kammala.

Duniyar kimiyya: Masana sun tabbatar da gano wani abun mamaki a duniyar wata
Duniyar kimiyya: Masana sun tabbatar da gano wani abun mamaki a duniyar wata

KU KARANTA: Masana sun gano illar yin wanka kullum

Masanan dai sun bayyana cewa wasu wuraren a saman duniyar wata inda rana bata haskawa sanyin wurin yakan kai har ma'aunin yanayin sanyi na digiri Selshios 157.

Legit.ng ta samu cewa wannan binciken na masana daga kasar Amurka dai na zaman tamkar wani mataki da suka sha alwashi na tabbatar da gano ko za'a iya yin rayuwa a saman duniyar ta wata.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa tun shekarun baya turawan yamma suke zuwa duniyar watan domin bincike amma sai dai har yanzu babu wanda ya taba zuwa ya dade domin kuwa yanayin duniyar ba zai bari ayi rayuwa ba a cikin ta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng