Kwankwaso ya maida martani game da kalaman Ganduje na shigar sa Kano

Kwankwaso ya maida martani game da kalaman Ganduje na shigar sa Kano

Tsohon gwamnan Kano kuma Sanata a halin yanzu dake wakiltar jihar a majalisar dattijai, Sanata Rabi'u Musa Kwankwanso ya bayyana kalaman Gwamna Ganduje na cewar ba zai iya shiga Kano ba a matsayin abun dariya.

Sanata Kwankwaso ya yace gwamna Ganduje yaron dan siyasa ne da ba zai iya fitowa yayi siyasa da kafafun sa ba sai ya labe bayan Shugaba Buhari domin yasan bai da magoya baya.

Kwankwaso ya maida martani game da kalaman Ganduje na shigar sa Kano
Kwankwaso ya maida martani game da kalaman Ganduje na shigar sa Kano

KU KARANTA: PDP ta gwalashe Kwankwaso

Legit.ng ta samu cewa Sanatan yayi wadannan kalaman ne a ta bakin mai magana da yawun sa Kwamared Abdulsalam inda ya kuma ce Gandujen yanzu haka a firgice yake saboda batun shigar ta Kwankwanso a garin na Kano.

A wani labarin kuma, Yayin da zabukan gama gari na shekarar 2019 ke cigaba da karatowa, babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta Peoples Democratic Party (PDP) ta babbayana cewa ba za ta kebance neman tikitin takarar wanda zai gwabza da shugaba Buhari a inuwar ta ba ga yankin Arewa maso yammacin Najeriya.

Wannan martanin dai na zaman tamkar gwalashewa ne ga tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanata dake wakiltar mazabar jihar Kano ta tsakiya a majalisar dattijai game da shawarar da ya bata a farkon makon nan inda ya shawarci jam'iyyar da ta bada tikitin takarar shugaban kasar ta ga wanda yafito daga yankin na Arewa maso yammacin Najeriya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel