Wani Kirista yayi wa musulmai sha-tara ta arziki a garin Kalaba

Wani Kirista yayi wa musulmai sha-tara ta arziki a garin Kalaba

Tsohon ministan al'adu da yawon bude ido a Najeriya kuma dantakarar kujerar Gwamnan jihar Kuros Ribas a zaben 2019 mai zuwa Mista Edem Duke ya yiwa musulmai musamman Hausawa da fulani na jihar da ke zaune a garin Kalaba, sha-tara ta arziki.

Mista Duke, kamar yadda muka samu dai daga majiyarmu ya ba al'ummar ne dake a zaune a unguwar Bagobiri a cikin garin Kalaba, babban birnin jihar buhunnan siminti har guda 200 a matsayin gudummuwar sa ga masallacin da suke ginawa.

Wani Kirista yayi wa musulmai sha-tara ta arziki a garin Kalaba
Wani Kirista yayi wa musulmai sha-tara ta arziki a garin Kalaba

KU KARANTA: Tun da na bar APC nike fuskantar matsaloli - Wani Gwamna a Arewa

Legit.ng ta samu cewa ya basu simintin ne da safiyar yau lokacin da ya ziyarce su don yayi masu barka da Sallah da kuma addu'a kammala shagulgulan sallah babba lafiya.

Da yake maida martan a madadin al'ummar yankinshugaban jam'iyyar APC na mazabar, Aminu Bin Usman ya yabawa dan takarar bisa ga gudummuwar da ya bada tare da yi masa alkawarin boyon baya.

A wani labarin kuma, Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake yaki da masu yiwa tattalikin kasa zagon kasa watau EFCC a takaice ta shigar da kara a wata babbar kotu dake a garin Legas akan wani Sanata daga jihar Akwa Ibom game da almundahana ta wasu makudan kudade.

Kamar yadda muka samu Sanatan mai suna Albert Bassey EFCC na tuhumar sa ne da laifin ansar cin hancin motoci 12 da kudin su ya kai Naira miliyan 254 daga hannun wani dan kasuwa a lokacin yana kwamishinan kudi a jihar ta Akwa Ibom.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel