Kwamacala: Wata uwa ta aure dan ta, tace bata bari wata can taci moriyar sa

Kwamacala: Wata uwa ta aure dan ta, tace bata bari wata can taci moriyar sa

Duniyar nan dai cike take labarai kuma idan har da sauran numfashin ka, to fa tabbas baka gama gani ko jin abun al'ajabi ba daga ko'ina daga fadin duniya.

Wani labari mai kama da almara da ya girgiza duniya shine na wata mata yar kasar Malawi dake a nahiyar Afrika da ta auri dan ta mai shekaru 30 a duniya har ma kuma da bayyana dalilin ta na yin hakan.

Kwamacala: Wata uwa ta aure dan ta, tace bata bari wata can taci moriyar sa
Kwamacala: Wata uwa ta aure dan ta, tace bata bari wata can taci moriyar sa

KU KARANTA: Tunda na bar APC nike ta fuskantar matsaloli - wani gwamna a Arewa

Matar dai mai suna Memory Njamani wadda ke da shekaru 47 a duniya na bayyana cewa ta yanke shawarar auren dan na ta ne biyo bayan wani dogon nazari da tayi akan irin wahalar da ta sha wajen dawainiya da shi har ya zama mutum.

Matar ta kara da cewa a don haka ne ma dai ta yanke shawarar cewa gaskiya ba za ta bari wata can ta mori dan na ta ba kara ita ta aure abin ta.

Memory Njamani dai ta kara da cewa duba da irin wahalhalun da ta sha akan dan nata tun daga raino da tarbiyya har zuwa ilimin sa, ta yanke shawarar cewa ita zata aure kayan ta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel