Soyayya ruwan zuma: Yadda wasu masoya suka kwashi 'yan kallo a jami'ar Bayero ta garin Kano (Bidiyo)

Soyayya ruwan zuma: Yadda wasu masoya suka kwashi 'yan kallo a jami'ar Bayero ta garin Kano (Bidiyo)

Wani faifan bidiyo da yayi ta yawo a kafafen sadarwar zamani da kuma ya dauki hankalin jama'a da dama musamman ma a arewacin Najeriya na dauke ne da yadda wani soja ya nunawa budurwar sa kauna a gaban jama'a a jami'ar Kano.

Bidiyon dai ya nuna sojan sanye da kakin sa da ake kyautata zaton soyayya suke da budurwar ya durkusa a gaban ta yana rokon ta amince da soyayyar sa.

Soyayya ruwan zuma: Yadda wasu masoya suka kwashi 'yan kallo a jami'ar Bayero ta garin Kano (Bidiyo)
Soyayya ruwan zuma: Yadda wasu masoya suka kwashi 'yan kallo a jami'ar Bayero ta garin Kano (Bidiyo)

KU KARANTA: Buhari zai dawo Najeriya yau

Legit.ng ta samu cewa saurayin a cikin wani irin salo na koyi da turawa, ya fiddo zobe daga aljihun sa inda ya kuma bukaci budurwa da ta mika hannun ta domin ya saka mata.

Sai dai budurwar wacce take a cikin shiga ta hausawa sanye da doguwar riga da kuma jan gyale ta fashe da kukan murna ne inda ta ma kasa hada ido da shi.

Lamarin dai ya auku ne a gaban tsangayar koyon ilimin lauya ne dake a jami'ar Bayero dake Kano kuma dalibai da dama sun shaida aukuwar lamarin.

Ga dai bidiyon nan:

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel