Sojoji sun kashe wani gawurtaccen dan fashi da makami tare da kwato makamai (Hotuna)

Sojoji sun kashe wani gawurtaccen dan fashi da makami tare da kwato makamai (Hotuna)

- Kwanan rikakken dan fashin nan da ya gallabi jama'a ya kare

- Bayan musayear wuta da Sojoji, 'yan fashin suka arce amma jami'an Sojin suka bi su

Wasu rahotanni sun bayyana cewa jami'an rundunar Sojin Najeriya sun yi musayar wuta a wani daji tare da wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne bayan sun yi musu kwanton bauna.

Inda suka samu nasarar kashe wani gawurtaccen dan fashi da makami nan da ya addabi al’umma mai suna Danbuzuwa, tare kuma da kwato wasu muggan makamai.

Sojoji sun kashe wani gawurtaccen dan fashi da makami tare da kwato makamai (Hotuna)
Sojoji sun kashe wani gawurtaccen dan fashi da makami tare da kwato makamai (Hotuna)

Cikin wata sanarwa da mataimakin kakakin rundunar Sojojin kasar nan Kanal Muhammad Dole ya sanyawa hannu, ta bayyana cewa rundunar Sojin ta rasa jami'inta daya da jikkatar wadansu guda 2 yayin artabun.

Sojoji sun kashe wani gawurtaccen dan fashi da makami tare da kwato makamai (Hotuna)
Sojoji sun kashe wani gawurtaccen dan fashi da makami tare da kwato makamai (Hotuna)

KU KARANTA: Kalli hotunan hazikan jami’an da suka kashe wata fitinanniyar gobara a Legas

Muhammad Dole ya kara da cewa bayan nasarar hallaka Sani Danbuzuwa, akwai kuma wasu ‘yan fashin guda 5 da aka samu nasarar hallaka su.

Tun da farko dai rundunar Sojojin kasar nan ta samu kiran gaggawa cewa akwai ‘yan fashi da makami akan hanyar Funtua zuwa Birnin Gwari, inda suka garzaya domin dakilewa tare da kame ‘yan fashin, akan hanyar tasu ne ‘yan fashin suka yi musu kwanton bauna, wanda hakan ya janyo yin artabu a tsakaninsu.

Bayan an yi musayar wutar ne sai ‘yan fashi da makamin suka arce zuwa cikin dajin Kuyambana dake jihar Zamfara.

Kawo yanzu dai jami'an Sojin da suka samu rauni na kwance a asibitin Sojoji dake Kaduna domin karbar magani.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng