Babban sakataren tarayya, Boss Mustapha tare da Akpabio sun ziyarci Aliyu Wamakko a gidansa dake Abuja (hotuna)
Babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mutspha, tare da tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio sun gana Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko.
Sun ziyarci Sanata Wamakko ne a gidansa dake babban birnin tarayya Abuja a daren ranar Talata, 14 ga watan Agusta.
Babu cikakken rahoto akan abunda suka tattauna a tsakaninsu ai dai ba zai rasa nasaba da halin da siyasar kasar ke ciki ba.
Ga hotunan ziyarar a kasa:
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin jihar Kaduna ta zabi sabon mataimakin kakakin majalisa
Tun bayan da Sanata Akpabio ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki yake rangaji wajen ziyartan manyan jiga-jigan jam’iyyar ta APC.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng