Wasu tsageru sun wawushe kudin sadakar da aka tara a wurin bauta
- 'Yan kungiyar asiri sun kaiwa wani malamin addini hari sun kwashe duk kudin addu'ar da aka tara
- Ana kyautata zaton cewa tsagerun mambobin daya daga cikin kungiyoyin asirin da suka addabi yankin ne
Fastor Suoyo dake wata Majami'a a jihar Bayelsa ya gamu da gamonsa, jim kadan bayan kammala karbar kudaden addua daga hannun wasu, inda yayi gamo da wasu tsageru ‘yan kungiyar asiri.
Malamin ya kammala addu'o'insa kamar kullum a kan hanyarsa ta zuwa gida yayi kicibis da azzaluman tsagerun.
A satin da ya gabata dai an samu karuwar wadannan muggan ayyuka na ‘yan kungiyar asiri a jihar, musamman ma a daidai kasuwar Swali.
Cikin makon da ya gaba ne aka samu barkewar rikici a tsakanin wasu kungiyoyin asirin inda suka yi dauki ba dadi a tsakaninsu har suka salwantar da rayukan wasu daga cikinsu.
KU KARANTA: Manyan jami’an INEC 3 da ake zargi da cin hanci sun samu beli kan Naira N300m
Ko a ranar Lahadin makon da ya gabata ma sai da suka tare hanya inda suka yi wa mutane da dama kwacen wayoyin hannu, agogon hannu, jakar hannu ta mata da sauran dukiyoyin jama'a.
Faston ya ce "Na baro coci akan hanyata ta zuwa gida kamar kullum, kawai sai muka yi kicibis da su, suka tare ni kuma suka caje ne tare da kwashe kudin mutane na addua har Naira dubu 8,355. Amma ina rokon ubangiji ya yafe musu".
Muyagun ayyuka da suka shafi kwace, garkuwa da mutane da kuma ‘yan kungiyar asiri yayi tsamari musamman a yankin na Swali, hakan ta sa mutanen yankin suka yi kira ga gwamnati da kuma masu ruwa da tsaki akan harkokin da suka shafi tsaro da su kawo musu dauki.
Wani mazaunin yankin wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda tsoron abinda ka iya zuwa ya dawo, ya ce "Da yawa daga yaran dake wannan mummunan aikin mun san su, amma ba zamu iya bayyanawa jami'an ‘yan sanda ba saboda tabbas zasu bayyana sunayenmu, kuma in har hakan ta kasance kashinmu ya bushe".
Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng