Bayan kwanaki 9 yana bacci, mai garkuwa a mutanen da ya sha Tramol ya sheka lahira
Hukumar yan sandan jihar Ondo ta sanar da cewa wannan mai garuwa da mutanen da ya sha Tramadol ya koshi a garin Owo ya sheka lahira bayan kwanaki 8 yana bacci bai tashi ba.
Hukumar dillancin labaran Najeriya ta bada rahoton cewa mai garkuwa da mutanen ya fara bacci ne tun ranan 5 ga watan Agustan da aka damkeshi a wani shago a jihar.
Kakakin hukumar yan sandan jihar, Mr Femi Joseph, ya alanta labarin mutuwarsa ne yayinda yae magana da manema labarai ranan Talata a gain Akure.
Game da cewar Joseph, ya mutu ne a babban asibitin Owo inda aka kaishi domn farfado da shi.
Yace: “ Ya mutu kwanaki tara da kamashi; munyi zaton zai tashi ne domin taimakawa bincikenmu, amma yam utu jiya(Litinin). Ana kyutata zaton cewa yawan Tramol da ya shane ya hallakashi.”
Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Wani mai garkuwa da mutane da har yanzu ba'a san sunansa ba yana hannun hukumar yan sandan jihar Ondo kuma har yanzu yana barci a ofishin hukumar.
KU KARANTA: APC na bukatar ‘Yan Majalisa 73 kafin ta iya tsige Saraki inji Lauyoyi
Jami'an yan sandan jihar sun damkeshi ne ranan Lahadi yayinda shi da abokansa uku sukayi kokarin garkuwa da wani mai shago a garin Owo.
Game da cewar hukumar yan sanda, matasan sun fasa wani shago ne da bindigogi domin garkuwa da mai shagon amma basu samu nasara ba, sai sukayi kokarin arcewa ta bayan gida.
Daya daga cikinsu yayi kokarin guduwa kan babur amma ya fara tangadi yayinda yake kokarin tayar da babur kuma ya fara bacci.
Sauran abokan aikinsa sun sha. Jami'an yan sandan sun ga kwayar Tramadol 400mg a cikin aljihunsa wanda yasa ake kyautata zaton cewa ya sha kwayar kafin zuwa aikin.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng