Daurin boye a 2019: Kwankwanso da gwamna Wike na jihar Rivers sun yi wata ganawar sirri

Daurin boye a 2019: Kwankwanso da gwamna Wike na jihar Rivers sun yi wata ganawar sirri

- Manyan 'yan siyasa na cigaba da tattaunawa don nemo hanyar da zata bulle musu

- Rabiu Musa Kwankwaso ya shiga ganawa da gwamnan jihar Rivers

- Daga cikin batutuwan da ake hasashen sun tattauna ya kunshi zaben 2019

Mai neman tikitin takarar shugabancin kasar nan karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Dakta Rabiu Musa Kwankwanso tare da gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, suna wata ganawar sirri a fadar gwamnatin jihar a yau Litinin.

Daurin boye a 2019: Kwankwanso da gwamna Wike na jihar Rivers sun yi wata ganawar sirri
Daurin boye a 2019: Kwankwanso da gwamna Wike na jihar Rivers sun yi wata ganawar sirri

Kwankwanso dai ya samu rakiyar tsohon gwamnan jihar Edo Lucky Igbinedion, tare da tsohon mai bawa shugaban kasa shawara akan harkar tattalin arziki. Dakta Magnus Kpakol sai kuma wasu da suke cikin jerin tafiyar shi Kwankwanson.

Kwankwanso ya jinjinawa gwamnan sannan ya bayyana cewa yana da kyau mutanen jihar su sake zabar Wike a karo na biyi domin karasa ayyukan alherin da debowa jihar.

KU KARANTA: Kalli hotuna da bidiyon yadda ruwa ya tafka gyara a Legas

"Muna rokon Allah ya bamu aron rai da lafiya domin ganin yadda zaka dawo a karo na biyu, sannan da cigaba da gina wannan jiha" inji Kwankwanso.

Tsohon gwamnan Kanon, ya yi amfani da ziyarar tasa wajen jajantawa al'ummar jihar bisa rasuwar tsohon Atoni janar Hon. Emmanuel Aguma (SAN).

Shi ma ana sa jawabin gwamnar jihar, ya bayyana rasuwar tsohon Atoni janar din a matsayin babban rashi da jihar tayi dama jam'iyyar PDP baki daya.

Gwamnan ya kara da cewa yayi matukar farin ciki da Kwankwanso ya dawo jam'iyyar PDP, Inda ya bayyana Kwankwanso dan siyasa mai nagarta wanda zai ciyar da jam'iyyar tasu ga gaci.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng