Dandalin Kannywood: Zainab Indomie ta fadi dalilin dusashewar tauraruwar ta
Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood watau Zainab Abdullahi da aka fi sani da Zainab Indomie ta sanar da dawowar ta harkar fim gadan-gadan bayan kusan hutun dole da ta dauka na shekaru biyar.
Zainab din dai ta bayyana hakan ne a shafin ta na dandalin sada zumunta na Instagram inda kuma ta ce ta samu tangarda a rayuwar ta ne biyo bayan kaiwa makura da tayi tun a farkon shekarun kuruciyar ta.
KU KARANTA: Malaman Arewa su shirya yadda za su kawo karshen Shi'a a yankin
Legit.ng ta samu cewa jarumar dai ta roki Allah ya yafe mata dukkan kura-kuran da ta aikata a baya da wanda ta sani da wanda ma bata sani ba domin a cewar ta yanzu ta bude sabon shafi ne a rayuwar ta.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa a baya jarumar tayi fice a masana'antar sosai kuma a cikin kankanin lokaci wanda hakan ne ma janyo mata dubban masoya da kuma makiya da dama.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng