Babbar Magana: Birkila ya haura gidan gwamnati ya saci kayan jami’an tsaro

Babbar Magana: Birkila ya haura gidan gwamnati ya saci kayan jami’an tsaro

- Dubun wani barawo da ya haura yayi sata gidan gwanatin jihar Oyo ya cika

- Tun tuni idonsa ya raina fata bayan da alkali ya ingiza keyarsa gidan kaso

Wata kotun Majistiri dake zamanta a kan titin Iwo na garin Ibadan ta yankewa wani magini hukuncin zaman gidan kaso har na tsawon watanni shida, bayan kama shi da laifin satar wasu kaya a gidan gwamnatin jihar Oyo dake yankin Agodi, wanda darajarsu ta kai Naira dubu N535,000.

Babbar Magana: Birkila ya haura gidan gwamnati ya saci kayan jami’an tsaro
Babbar Magana: Birkila ya haura gidan gwamnati ya saci kayan jami’an tsaro

‘Dan sanda mai ganatar da kara Sunday Ogunremi, ya bayyanawa kotun cewa mai laifin ya samu damar haura katangar gidan gwamnatin ne tare da shiga yankin jami'an ‘yan sanda inda ya saci kadarorin.

KU KARANTA: ‘Yan sanda sun cafke wani Saurayi da kwarangwal din kan mutune 3

Kotun ta bayyana kayan da ya sata wanda daga ciki suka hada da; Agogon hannu, rigunan sawa guda hudu, wanduna, da kuma wasu kayan jami'an jami’an da suke cire bam (Anti-Bomb squad) wanda ake yi kiyasin sun kai Naira dubu 534,000.

Kotun dai ta yanke masa hukunci karkashin sashi na 411 da 390 (9) na kundin laifuka na jihar ta Oyo na shekarar 2000.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng