Fasahar kirkira: Wani matashi daga Arewa ya kerawa sojin Najeriya jirgin yaki
Wani labari da mukayi kicibis da shi mai dadin gaske ga dukkan 'yan arewa shine na wani hazikin matashi daga garin Rigasa ta jihar Kaduna wanda ya kirkira tare da kerawa rundunar sojin saman Najeriya jirgin yaki.
Kamar yadda muka samu, matashin ya nunawa sojojin jirgin mai dauke da kalar tutar Najeriya da ya kirkira masu tare da hannata masu shi a garin Maiduguri.
KU KARANTA: Wani abun alheri ya sanu Maryam Sanda
Legit.ng ta samu cewa ko da dai bamu samu sunan hazikin matashin ba, amma wanine dake kyautata zaton aminin sa ne ya wallafa hotunan sa mai suna Dud Malumfashi a shafin sa na Fesbuk.
Matasan arewacin Najeriya dai na da matukar fasaha musamman ma ta kere-kere inda akan same su sun yi fice a dukkan abunda suka kera hatta ma a dandamalin duniya.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng