Yanzu-yanzu: Saraki yana ganawar sirri da Obasanjo
Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya shiga ganawar sirri da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Saraki ya isa gidan Obasanjo da yammacin yau Litinin, 13 ga watan Agusta, 2018.
A makon da ya gabata, shugaban majalisar dattawan ya yi irin wannan ganawar da tsohon shugaban kasa, Ibrahim Babangida, a gidansa dake Minna, jihar Neja.
Ganawar Saraki da wadannan tsaffin shugabannin na da alaka da dambarwan siyasar Najeriya musamman yanzu da ake fuskantar 2019. Kana barazanar tsigewa da yake fuskanta a majalisar bayan sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP.
KU KARANTA: masu zanga-zanga sun kunyata Kwankwaso sunyi masa ihun ‘Sai Buhari’ a filin jirgi
Kamar yadda aka sani, tsohon shugaba Obasanjo da Babangoda sun bayyana rashin amincewarsu da gwamnatin Buhari kuma sun lashi takobin kawo karshen gwamnatin a 2019.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng