Yanzu Yanzu: Kotun daukaka kara ta dakatar da kama shugaban INEC, Mahmood

Yanzu Yanzu: Kotun daukaka kara ta dakatar da kama shugaban INEC, Mahmood

Kotun daukaka kara dake Abuja ta dakatar da umurnin kama shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, Mahmood Yakubu da Justis Stephen Pam na babban kotun tarayya ta bayar.

Kwamitin mutum 3 karkashin jagorancin Justis Abdul Aboki ta dakatar da umurnin kamun a wani hukunci da aka yanke a ranar Litinin, a daukaka karar da Farfesa Mahmood yayi inda ya kalubalanci umurnin Justis Pam na cewa a kama shi.

Yanzu Yanzu: Kotun daukaka kara ta dakatar da kama shugaban INEC, Mahmood
Yanzu Yanzu: Kotun daukaka kara ta dakatar da kama shugaban INEC, Mahmood

Justis Aboki ya bayyana cewa tunda a dage sauraron lamarin zuwa ranar 17 ga watan Satumba “zai zamo son zuciya kan cigaba da sauraron lamarin a ranar 14 ga watan Agusta."

KU KARANTA KUMA: Za mu kai mamaya maJalisar dokokin kasar idan Saraki yaki yin murabus – Kungiyar yakin neman zaben Buhari

A baya Legit.ng ta rahoto cewa rundunar yan sanda za ta kama shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Yakubu Mahmood a gaban kotu a gobe bisa ga umurnin Justis Stephen Pam na babbar kotun tarayya dake Abuja.

A ranar Laraba da ta gabata ne kotu nta same bada umurni ga yan sanda cewa su kama sannan su gurfanar da shugaban INEC a gaban kotu bayan rashin hallara da baiyi ba a kotu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng