2019: An sanyawa Dankwambo zafi cewa ya hakura ya barwa Tambuwal takara

2019: An sanyawa Dankwambo zafi cewa ya hakura ya barwa Tambuwal takara

Alamu sun nuna a jiya cewa an sanyawa gwamnan jihar Gombe kuma dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin lemar Peoples Democratic Party (PDP), Ibrahim Hassan Dankwambo, zafi cewa ya hakura da kudirinsa gabannin zaben fid da gwani na jam’iyyar.

Legit.ng ta tattaro cewa Dankwambo waanda ya bayyana kudirinsa na son takarar shugaban kasa makonni biyu da suka shige na fuskantar matsin lamba daga wasu shugabannin siyasa da sarakuna a yankin arewacin kasar kan ya hakura ya barwa gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal.

Ku tuna cewa Tambuwal, wanda ya kasance tsohon kakakin majalisar wakilai na daya daga cikin manyan yan siyasan da suka sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa PDP a kwanan nan.

2019: An sanyawa Dankwambo zafi cewa ya hakura ya barwa Tambuwal takara
2019: An sanyawa Dankwambo zafi cewa ya hakura ya barwa Tambuwal takara

Bincike sun nuna cewa dalilin zabar Tambuwal ya kasance saboda yakinin cewa yana da dunbin magoya baya a fafutukar fiye da Dankwambo.

Majiyoyi na kusa da gwamnan sun fadawa majiyarmu ta Leadership cewa sakamakon matsin lamba da yake samu da kuma goyon bayan da aka ba Tambuwal a yanzu, Talban Gomben na duba ga neman takarar kujerar sanata na Gombe ta arewa.

KU KARANTA KUMA: Malaman Arewa sun shirya yadda za su kawo karshen shi'a

Masu kira ga hakan na ganin fitar da mutum kamar Tambuwal wanda ya fito daga yanki daya da shugaban kasa Muhammadu Buhari wato arewa ta yamma zai bada nasarar kayar da shugaban kasar cikin sauki.

Sai dai a yammacin ranar Lahadi, 12 ga watan Agusta gwamna Dankwambo ya karyata cewar yana fuskantar matsin lamba game da hakura ya barwa Tambuwal.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng