Malaman Arewa sun shirya yadda za su kawo karshen shi'a

Malaman Arewa sun shirya yadda za su kawo karshen shi'a

Wasu malaman addinin musulunci a arewacin Najeriya a ranar Lahadi sun yi wani taro a garin Kaduna inda suka koka tare da yin tir da mabiya tafarkin shi'a almajiran Zakzaky watau Islamic Movement in Nigeria (IMN).

Malaman dai sun yi taro ne na kaddamar da wani littafin da shehin malami Farfesa Umar Labdo na jami'ar Maitama Sule dake garin Kano ya rubuta game da akidun shi'a da kuma dabi'o'in su da ya bayyana a matsayin marasa kyau kuma abun kyama.

Malaman Arewa sun shirya yadda za su kawo karshen shi'a
Malaman Arewa sun shirya yadda za su kawo karshen shi'a

KU KARANTA: Da dumin sa: An ga gawar wani hadimin gwamna a dakin sa

Legit.ng ta samu cewa shima babban sakataren kungiyar Jama'atunnasrul Islam Dakta Khalid Aliyu Abubakar ya bayyana kungiyar a matsayin abun kyama sannan kuma ya bukaci hadin kan jama'a domin ganin an kawo karshen ta.

Daga karshe dai malaman sun yi ittifakin cewa da ilimi ne ta kuma hanyar wayar ma da al'umma kai da irin litattafai makamantan wadan nan ne za a iya kawo karshen na shi'a a yankin na arewa

A wani labarin kuma da muke samu daga majiyoyin mu na nuni ne da cewa an ga gawar daya daga cikin hadiman Gwamnan jihar Anambra Willie Obiano kuma mai taimaka masa na musamman mai suna Mista Randie Chima a dakin sa.

Majiyar ta mu dai ta tabbatar mana da cewa a ranar Juma'a hadimin gwaman yayi ta hidimar sa lafiya lau kuma har ma yaje wani wurin shagali da daren juma'ar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel