Batan-baka-tantan: Jiga-jigan jam'iyyar APC a Akwa Ibom sunce basu son Akpabio

Batan-baka-tantan: Jiga-jigan jam'iyyar APC a Akwa Ibom sunce basu son Akpabio

Wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyar adawa a jihar Akwa Ibom ta All Progressives Congress, APC sun fito sun nuna kin amincewar su ga zaman tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar dattijan kasar nan Sanata Godswill Akpabio jagoran jam'iyyar.

Daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar dai da yayi magana a madadin su, Emmanuel Sam ya bayyana cewa za su yi anfani da dukkan karfin su wajen ganin ba'a mika jam'iyyar a hannun sa ba.

Batan-baka-tantan: Jiga-jigan jam'iyyar APC a Akwa Ibom sunce basu son Akpabio
Batan-baka-tantan: Jiga-jigan jam'iyyar APC a Akwa Ibom sunce basu son Akpabio

KU KARANTA: Budurwa ta yanke zakarin saurayin ta a Jigawa

Legit.ng ta samu cewa haka zalika Mista Sam ya kara da cewa idan har aka ba shi jagorancin jam'iyyar ta tabbas rushewar su ta zo domin kuwa daman can shine ya kori jama'a daga tsohuwar jam'iyyar sa.

A wani labarin kuma, Tsohon mukaddashin gwamna a jihar Adamawa dake a arewacin Najeriya kuma na hannun gwamnan jihar Umaru Jibrilla mai suna Ambasada James Barka ya sanar da ficewar sa daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Da yake tabbatar da ficewar tasa daga jam'iyyar, Mista Barka ya bayar da dalilai na rashin kyautawar gwamnan jihar da kuma rashin gaskiyar da ake tafkawa a gwamnatin a matsayin musabbabin ficewar ta sa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng