Gudun tsira da mutunci na ne yasa na yarda da kwallon mangwaro - Tsohon mataimakin gwamnan Kano
- Bayan sauka daga mukaminsa na mataimakin gwamnan Kano, Farfesa Hafiz yayi wasu batutuwa
- Daga cikin maganganun da yayi har da bayanin yadda aka rika tauye masa hakkokin da ya kamata ana ba shi a matsayinsa na mataimakin gwamna
Tsohon Mataimakin gwamnan jihar Kano Farfesa Hafiz Abubakar, wanda ya gabatar da takardar murabus dinsa a makon da ya gabata, ya zargi gwamna Abdullahi Umar Ganduje da zalunci da tauye masa hakkin gami da mayar da shi saniyar ware.
Farfesan tabbatar da cewa rashin bashi hakkin da kundin tsarin mulkin kasar nan ya tanadar masa shi ne bdalilin da ya sanya shi yin murabus daga kujerar mataimakin gwamnan.
Farfesa Hafiz ya bayyana hakan ne a cikin wata tattaunawa da jaridar PUNCH ta yi da shi, ya kara da cewa fiye da shekara biyu, zaman doya da manja ake yi tsakaninsa da gwamna Ganduje saboda yana ra'ayin Kwankwasiya. Har ta kai ana yiwa rayuwarsa barazana.
Tsohon mataimakin gwamnan, ya ce ya so ya ci gaba da rike mukaminsa har zuwa karshen wa'adin mulkin da aka zabe su, amma ya sauka ne saboda matsalolin da suka dabaibaye dangantakarsa da gwamnan jihar.
KU KARANTA: 'Yan majalisar Kano sun shirya yiwa Ganduje Tutsu, za su koma PDP
Farfesa Hafiz ya ce da kudinsa yake yiwa gwamnatin Kano duk wata hidima da ya ke yi mata.
Sannan ya zargin cewa duk abinda ake yi masa ana yi masa saboda alakarsa da Kwankwaso.
A karshe ya bayyana goyon bayansa ga Sanatan Kano ta tsakiya Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, akan kudurinsa na takarar shugabancin kasar a tutar jam’iyyar PDP.
Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng