Zaben jihar Katsina: Mutane sun fito kwansu da kwarkwatan domin zaben yan gida daya

Zaben jihar Katsina: Mutane sun fito kwansu da kwarkwatan domin zaben yan gida daya

- INEC ta kaddamar da zaben Kastina ta Arewa domin maye gurbin kujeran a majalisae dattawa

- Ana gudanar da wannan zabe ne sakamakon rasuwar Sanata Mustapha Bukar wanda ke wakiltan mazabar

- Mukaddashin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, a ranan Alhamis ya garzaya Daura domin yakin neman zaben jam'iyyar APC

An fara zaben kujerar sanatan Katsina ta Arewa cikin zaman lafiya da lumana a kananan hukumomi 12 da ke karkashin mazabar a ya Asabar, 11 ga watan Agusta 2018.

Legit.ng ta samu labarin cewa hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC sun kaddamar da zaben kuma mutane sun fito kwansu da kwarkwatansu.

Game da cewar NAN, an fara tantance masu zabe misalin karfe 8:00 na safe kuma jami'an INEC sun isa da wuri.

KU KARANTA: An samu biliyoyi, manyan bindigu da dubban katinan zabe a gidan Lawal Daura

Mutane sun fito kwansu da kwarkwatnsu domin zabe tsakanin yan gida daya dake takarar kujera daya. Kabir Babba Kaita na jam'iyyar PDP da kaninsa, Ahmad Babba Kaita na jam'iyyar APC

Wani dan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya yabawa hukumar INEC bisa ga isowarsu da wuri. Yace an fara zabe a unguwanni 148 da ke mazabar a lokaci daya.

Mazabar Katsina ta Arewa ya kunshi kananan hukumomi Daura, Maiadua, Zango, Sandamu, Baure, Mani, Mashi, Dutsi, Ingawa, Bindawa, Kankiya da Kusada.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel