Mutuwa rigar kowa: An bude kantin hirar mutuwa a birnin Legas

Mutuwa rigar kowa: An bude kantin hirar mutuwa a birnin Legas

Abun mamaki tabbas baya karewa kuma lallai ne idan dai har kana raye, to a kullum kara ilimi mutum ke yi a wannan duniyar tamu.

Wani lamarin da ya auku a kasar Najeriya kuma a birnin Legas dake a kudancin kasar shine na wani kanti da aka bude domin tattaunawa tare da labarin mutuwa kawai.

Mutuwa rigar kowa: An bude kantin hirar mutuwa a birnin Legas

Mutuwa rigar kowa: An bude kantin hirar mutuwa a birnin Legas

KU KARANTA: Jirgi mai saukar angulu yayi hadari da mutum 9

Kantin dai kamar yadda muka samu daga majiyar mu ta BBC Hausa, wani taro ne da aka shirya za'a rika yi a duk wata inda mutane za su taru su amayar da labarin mutuwar da ya tsaya masu a rayuwar su.

Legit.ng ta samu haka zalika cewa wadda ta kirkiri shawarar bude kantin mai cewa Hope Ogbologugo ta ce yana taimaka wa mutane su kara sanin kimar rayuwa.

Ta kara da cewa ce kafin ta bude kantin na mutuwa, ba ta iya magana a kan mutuwar mahaifiyarta amma yanzu tana iya yin hirar da mutane.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel