Zaben cike gurbi: Gwamnonin APC 4 sun garzaya Bauchi don marawa dan takara baya
Gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress ( APC) guda hudu na a jihar Bauchi a anz haka domin marawa dan takarar jam’iyyar, Lwal Yahaya Gumau baya domin lashe zaben cike gurbi a yankin Bauchi ta kudu.
Gwamnan jihar Zanfara wadda ya kasance shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Abdulazeez Yari ne ya jagorance su domin taya dan takarar kamfen na karshe.
Sauran gwamnonin sun hada da; Simon Lalong na Plateau, Atiku Bagudu na Kebbi da Badaru Abubakar na jihar Jigawa.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Dole a tsige Saraki - Oshimhole
Da yake Magana dan takarar APC, Lawal Yahaya Gumau, ya bayyana cewa yana son komawa majalisar dattawa daga majalisar wakilai domin kare martabar shugaban kasa Muhammadu Buhari, mazabarsa da kuma kasar sa.
A halin da ake ciuki, Adams Oshiomhole, shugaban jam’iyyar Progressives Congress (APC) na kasa, yace babu makawa sa an tsigeshugaban majalisar dattawa Bukola Saraki.
Da yake magana a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Juma’a, 10 ga watan Agusta, Oshiomhole yace bayan tsige Saraki jam’iyyar zata yi kokari don tabbatar da cewa an kayar da shi a mazabarsa a 2019.
Yace za’a lalata daular siyasar Saraki a jiha Kwara.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng