Sauyin sheka: Tsohon gwamna a Arewa da wasu jiga-jigan jam'iyyar APC na shirin komawa PDP

Sauyin sheka: Tsohon gwamna a Arewa da wasu jiga-jigan jam'iyyar APC na shirin komawa PDP

Labaran sirri da muke samu daga majiyar mu ta Daily Nigerian sun tabbatar mana da cewa wasu jiga-jigan jam'iyyar All Progressives Congress, APC a jihar Taraba na shirin sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki a jihar ta PDP.

Manuya daga cikin wadanda dai ke shirin sauya shekar kamar yadda muka samu sun hada ne da tsohon gwamnan jihar kuma Sanata dake wakiltar jihar a majalisar dattijai yanzu watau Sanata Sani Danladi da kuma Joel Ikenya da ma 'yan majalisun tarayya da na jiha da dama.

Sauyin sheka: Tsohon gwamnan a Arewa da wasu jiga-jigan jam'iyyar APC na shirin komawa PDP
Sauyin sheka: Tsohon gwamnan a Arewa da wasu jiga-jigan jam'iyyar APC na shirin komawa PDP

KU KARANTA: Ku zo kuga hotunan fadar shugaban kasar Najeriya ta Villa

Legit.ng ta samu cewa wannan bayanin sirrin dai ya fara fitowa fili ne biyo bayan wani zaman sirri da ''yan siyasar suka yi da gwamnan jihar Mista Darius Ishaku a masaukin sa na garin Abuja.

A wani labarin kuma, Dubun dubatar al'umma masoya tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanata a yanzu, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ne suka sauya sheka ya zuwa daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar PDP a jihar Edo.

Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu ta jaridar Vanguard, 'yan kwankwasiyyar sun sauya shekar ne tare da wasu mambobin bangaren nan na 'yan awaren jam'iyyar APC.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel