Zaben cike gurbi: An sanya dokar hana walwala a kananan hukumomi 7 a jihar Bauchi
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta sanar da sanya dokar hana walwala a kananan hukumomi bakwai a jihar.
Mai magana da yawun hukumar Kamal Abubakar ne ya sanar da haka ranar Alhamis, 9 ga watan Agusta.
A cewarsa an kafa wannan doka ne saboda a samu damar gudanar da zaben cike gurbin Bauchi ta Kudu da za a yi ranar Asabar cikin kwanciyar hankali da lumana.
Abubakar yace dokar za ta fara aiki ne daga ranar Juma’a 10 ga watan Agusta daga karfe 12 na dare zuwa karfe takwas sannan a ci gaba washe gari 11 ga watan Agusta.
Yankunan da dokar ya shafa sun hada da Bauchi, Toro, Alkaleri, Bogoro, Tafawa Balewa, Dass da Kirfi.
KU KARANTA KUMA: Wike ya bukaci Osinbajo da ya sallami shugaban EFCC
A karshe jami’in hukumar zabe na jihar Ibrahim Abdullahi ya yi kira ga duk jam’iyyun da su gaya wa magoya bayan su da su bi doka a lokacin zabe.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng