Magoya bayan Kwankwasiyya sun bar APC, sun cinnawa tsinsiya wuta a Nasarawa
Jiya magoya bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na kungiyar Kwankwasiyya Movement, a jihar Nassarawa, sun sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP.
Magoya bayan sanatan sun bayyana sauya shekarsu daga APC ne a sakateriyar PDP tare da kone-konen tsintsiya.
Kungiyar ta samu wakilcin Architect Aminu Dabo a madadin Sanata Kwankwaso.
Dabo yace dawowar Kwankwaso jam’iyyar PDP ya kasance sanadiyar rashin adalci a siyasa da kuma cin zarafin al’umma.
KU KARANTA KUMA: Shugaban R-APC Buba Galadima ya samu lafiya bayan yayi hadarin mota
Yayinda yake mayar da martani, shugban jam’iyyar PDP a jihar, Fransis Orgu, ya bada tabbacin cewa za’a ba wadanda suka sauya sheka dama a jam’iyyar da kuma karfafa su don rijista tare da PDP a kananan hukumomi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng