Haushin faduwa zabe: Tsohon minista ya cire fanfon tuka-tuka 10 da ya ginawa jama’ar sa

Haushin faduwa zabe: Tsohon minista ya cire fanfon tuka-tuka 10 da ya ginawa jama’ar sa

Wani tsohon minista day a fadi zaben zama mamba a majalisar kasa ya cire fanfon tuka-tuka 10 da ya ginawa jama’ar sa shekaru 20 da suka wuce.

Tsohon ministan, Patrick Okumu-Ringa, ya fadi zaben majalisa da aka kamala na kwana-kwanan nan a kasar Uganda. Patrick ya tsaya takarar zama dan majalisa mai wakilta birnin Nebbi ne.

Patrick ya mallaki kasa mai fadin gaske a birnin na Nebbi kuma ya gina fanfunan tuka-tuka 10 a wuri daban-daban domin taimakon jama’ar sa.

Haushin faduwa zabe: Tsohon minista ya cire fanfon tuka-tuka 10 da ya ginawa jama’ar sa
Fanfon tuka-tuka

Tsohon minista Patrick ya bayyana cewar ya cire fanfunan tuka-tukan ne domin jama’ar sa sun yi masa butulci ta hanyar kin bashi kuri’un da zasu bashi nasarar zama dan majalisa. An fara cire fanfunan tuka-tukan ne ranar Litinin, kwana 3 kacal bayan fitar da sakamakon zabe.

DUBA WANNAN: Ana kulla tuggun tsige Buhari - Tinubu

Patrick ne ya zo na 3 da kuri’u 1,270 a zaben da aka kammala. Abokin takararsa Hashim ne ya lashe zaben da adadin kuri’u 4,283 daga cikin jimillar kuri’u 9,940 da aka kada a zaben.

Da kudin aljihuna nayi amfani na gina masu fanfon tuka-tuka, yanzu sai gwamnati ta gina masu wasu tunda sun yi min butulci duk da sun san cewar ko gwamnatin kasar Uganda bata samar da ruwa ga jama’a kyauta,” a kalaman Patrick.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: