Sunaye da mukaman manyan jigogin PDP da zasu bi Akpabio zuwa jam’iyyar APC
- Jam'iyyar PDP na shirin rasa wasu jigoginta da suka daura niyyar bin Akpabio
- Tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom din shaida ficewarsa daga jam'iyyar har ya sauka daga mukaminsa na shugaban marasa rijaye a majalisar dattawa
- Har ya gana da shugaban kasa Muhammad Buhari a birnin Landan
Rahotanni sun bayyana cewa akwai wasu jiga-jigai na jam'iyuar PDP goma sha daya a jihar Akwa-Ibom da ake sa ran zasu fice daga jam'iyyar zuwa jam'iyyar adawa ta APC a yau laraba.
Sanata Godswill Akpabio, wanda tsohon gwamnan jihar ta Akwa-Ibom ne kuma Sanata mai ci a yanzu ya fice daga jam'iyyar tare da ajiye mukaminsa na shugaban marasa rinjaye a majalisar ta dattijai.
KU KARANTA: 2019: Bamu da wadda ya kai Buhari wajen sanyin hali – Kungiyar yakin zabe
Sunayen mutanen da ake sa ran zasu bi Sanatan Godswill Akpabio zuwa jam'iyyar APC su ne kamar haka:
1- Victor Antai - Kwamishinan al'adu da yawon bude ido.
2- Chief Michael Afangideh - Shugaban jam'iyya na jihar.
3. Don Etim - Tsohon kwamishinan aiyuka.
4. Godwin Afangideh - Mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na jihar ta Akwa-Ibom.
5. Ibanga Akpabio - Kwamishinan tsare-tsare da aiyuka.
6. Nse Ntuen - Dan majalisar jiha mai wakiltar Essien Udim
7. Gabriel Tobby - Dan majalisar jiha wai wakiltar Etim Ekpo/Ika
8. Raphael Isobara - Shugaban karamar hukumar Essien Udim
9. Unyime Etim - Shugaban karamar hukumar Ikot Ekpene
10. Emmanuel Akpan - Dan majalisar tarayya mai wakiltar Ikot Ekpene
11. Emmanuel Ekon - Dan majalisar tarayya mai wakiltar Etim Ekpo/Ika/Abak.
KU KARANTA:
A baya dai Legit.ng ta rawaito Sanata Akpabio ya samu gagarumar tarbar a jihar bayan da ya bayyana kudirinsa na komawa jam'iyyar APC.
Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng