Nada sabon Shugaban Majalisar Dattawa, Tantance Magu da abubuwan da ke daf da aukuwa a Najeriya

Nada sabon Shugaban Majalisar Dattawa, Tantance Magu da abubuwan da ke daf da aukuwa a Najeriya

Mun kawo maku jerin wasu abubuwan da ka iya faruwa a Najeriya cikin ‘yan kwanaki masu zuwa. Ba mamaki wadannan abubuwa su faru kafin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo daga hutun da ya tafi a Landan.

Nada sabon Shugaban Majalisar Dattawa, Tantance Magu da abubuwan da ke daf da aukuwa
Mukaddashin Shugaban kasa ya tsige Lawal Daura daga ofis

1. Tsige Bukola Saraki

Babu mamaki idan har an bude Majalisa ayi yunkurin tsige Bukola Saraki bayan ya koma Jam’iyyar PDP wanda ba ta da rinjaye a Majalisa. Jam’iyyar APC mai mulki tuni ta gama zawarcin Sanata Godswill Akpabio da ake tunani zai ja ragamar Majalisar Dattawan kasar.

KU KARANTA: Bukola Saraki ya isa zauren Majalisar Dattawan Najeriya

2. Tantance Shugaban EFCC

Idan har an nada wani sabon Shugaban Majalisar Dattawa, babu mamaki fadar Shugaban kasa ta kara aikawa Majalisar sunan Ibrahim Magu domin a tabbatar da shi a matsayin mukaddashin Shugaban EFCC. A baya dai Hukumar DSS ta nemi kar a dakatar da Magu.

3. Nadin sababbin mukamai da sauran su

Babu mamaki dai kafin Shugaban kasa Buhari ya dawo a nada sabon Shugaban DSS. Kuma da zarar an bude Majalisa, fadar Shugaban kasa za ta nemi a tabbatar da wasu nade-nade da ke gaban Majalisa. Akwai kuma batun kasafin kudin bana da ake sa rai a gama aikin sa.

Kun san cewa a halin yanzu mukaddashin Shugaban Kasa Osinbajo ya sallami Lawal Daura daga aiki. Tuni dai har an nada Matthew Seiyefa a matsayin wanda zai rike ofishin kafin a nada wani na din-din-din

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng