Yanzu Yanzu: Dogara ya isa majalisar dokoki, yan majalisar wakilai sun kasance cikin farin ciki
Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara kamar takwaransa, shugaban majalisar dattawa ya isa majalisar dokoki da misalin arfe 5:08 na yammacin ranar Talata, 7 ga watan Agusta bayan mamayar da hukumar DSS ta kai.
samu kyakyawar tarba daga yan majalisar dokoki inda suka shiga rera masa waka a lokacin da suka hange shi, jaridar The Punch ta ruwaito.
Shugaban kwamitin majalisa akan kasuwa, Tajudeen Yusuf da shugaban kwamitin asusun jama’a, Kingsley Chinda ne suka jagoranci yan majalisar a waka yayinda suka tafi gaishe da Dogara cikin gaggawa.
Kakakin majalisar ya maida masu da martani ta hanyar daga hannu da kuma gaisawa da wasu da dama daga cikinsu.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An janye jami’an tsaro daga majalisar dokokin kasar
Ya shige ofishin sa yayinda abokan aikinsa suka ci gaba da wake shi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng