FAAN ta gargadi yan siyasa da su bi ka’idar tsaro bayan mamayar da aka kai filin jirgin sama na Sokoto

FAAN ta gargadi yan siyasa da su bi ka’idar tsaro bayan mamayar da aka kai filin jirgin sama na Sokoto

Hukumar kula da filayen jiragen sama na Najeriya (FAAN) ta gargadi yan siyasa aka sabama tsarin tsaro a filayen jiragen sama, musamman yayinda zaben 2019 ke gabatowa.

Hukumar gwamnatin ta yi wannan gargadi bayan wasu magoya bayan siyasa sun karya dokar inda tsaro ta bayar da damar tsayawa sannan suka mamaye filin jirgin sama na Sultan Abubakar III ake jihar Sokoto a ranar Juma’a.

FAAN ta gargadi yan siyasa da su bi ka’idar tsaro bayan mamayar da aka kai filin jirgin sama na Sokoto
FAAN ta gargadi yan siyasa da su bi ka’idar tsaro bayan mamayar da aka kai filin jirgin sama na Sokoto

Aliyu Wamakko, tsohon gwamnan Sokoto kuma sanata mai wakiltan Sokoto ta arewa a yanzu, ya samu kyakyawar tarba daga dondozon magoya bayansa yayinda ya dawo gida.

KU KARANTA KUMA: Kwamishina da wasu mutane 4 na hararar kujerar mataimakin gwamnan Kano

A wata sanarwa daga babban manaja mai kula da harkokin FAAN, Henrietta Yakubu ya bayyana lamarin a matsayin abun Allah wadai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel