Fitar Saraki, Tambuwal da Ortum ba zai hana Buhari cin zabe ba - APC

Fitar Saraki, Tambuwal da Ortum ba zai hana Buhari cin zabe ba - APC

- Gaba kura baya yaki ga jam'iyyar APC mai mulki

- Amma sai dai har yanzu APC na nuna ko a jikinta wai an mintsini kakkausa

- Ta tabbatar da cewa ficewar jigogin nata ba wata matsala da zai haifar mata

Jamiyyar APC ta bayyana cewa ficewar shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kuma gwamnoni uku daga jam’iyyar ba zai kawo wani nakasu ga sake zaben shugaban kasa Muhammad Buhari ba.

Fitar Saraki, Tambuwal da Ortum ba zai hana Buhari cin zabe ba - APC

Fitar Saraki, Tambuwal da Ortum ba zai hana Buhari cin zabe ba - APC

Jawabin hakan ya fitowa ne daga bakin mai rikon mukamin kakakin jam’iyyar na kasa Yekini Nabena.

Nabena ya ce “Ina tabbatar muku cewa ficewar wadannan mutanen daga cikin jam’iyyar APC ba zai yi tasiri ga nasarar jam’iyyar APC ba. Kowa ya sani tasiri da farin jinin siyasar Bukola Saraki ya tsaya ne kawai a iya jihar kwara domin ko jihar kogi bai kai ba, balle a ce yana da tasirin siyasa a yankin arewa ta tsakiya, inda shugaba Muhammad Buhari yake da dubban magoya baya".

“Idan kuma kana maganar Aminu Tambuwal gwamnan jihar Sokoto, to babu shakka kowa ya san maigidansa wato Sanata Aliyu Wamakko ya fi shi yawan magoya a fadin jihar Sokoto, domin al'ummar kasar nan sun shaida dandazon al'ummar da suka fito su ka tarbe shi a ranar Asabar".

KU KARANTA: Tsaka mai wuya: APC da wasu jam'iyyu 15 sun yiwa Saraki taron dangi

Ya kara da cewa a jihar Sokoto suna da Mataimakin gwamna da ‘yan majalisar dattawa guda 2, da ‘yan majalisar wakilai guda 9, da kuma ‘yan majalisar dokokin jiha guda 12.

Da ya jiyo jihar Benue kuwa, mukaddashin kakakin ya bayyana cewa gwamna Samuel Ortom yana fama da rashin karbarsa da jam’iyyar PDP ta yi a jihar.

"Har Yanzu Samuel Ortom yana fuskantar matsala a cikin jam’iyyar PDP, domin kuwa kowa ya san tasirin da karfin siyasar tsohon gwamnan jihar a cikin jam’iyyar PDP wato Gabriel Suswam, wanda kuma yake da ragamar jam’iyyar a hannunsa, shi zai tsara yadda ya ke so. Amma Lokaci zai yi da zai nuna wa yake rike da siyasar jihar ta Benue" Yekini ya jaddada

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel